A yau Talata da safe ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci ofishin jakadancin kasar Cuba da ke nan birnin Beijing, inda ya mika ta'aziya game da rasuwar jagoran juyin-juya halin kasar ta Cuba marigayi Fidel Castro.
Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, ya bayyana Fidel Castro mutumin da ya kirkiro jam'iyyar Kwaminisanci ta Cuba kana mai kishin kasa, a matsayin babban jagoran al'ummar kasar Cuba.
Shugaba Xi ya ziyarci ofishin jakadancin kasar ta Cuba ne don nuna cewa, JKS, gwamnati da al'ummar kasar Sin suna tare da jam'iyyar kwaminis ta kasar Cuba, gwamnati da kuma al'ummar kasar a wannan lokaci mai muhimmanci.(Ibrahim)