A yau Litinin ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da mista Antonio Guterres, babban sakataren MDD mai jiran gado a birnin Beijing.
A yayin ganawarsu, shugaba Xi ya taya mista Guterres murnar zama babban sakataren MDD mai jiran gado, ya kuma jaddada cewa, Sin za ta ba shi dukkan goyon bayan da zai taimaka masa gudanar da aikinsa.
Haka kuma, shugaba Xi ya jaddada cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 45 da Sin ta samu kujerar dindindin a kwamitin sulhu na MDD. A cikin wadannan shekaru 45, Sin ta yi hadin gwiwa da MDD tare da samun sakamako mai kyau ta hanyar yin mu'amala tsakanin manyan jami'ansu, da karfafa mu'amala bisa manyan tsare tsare, da kuma inganta hakikanin hadin gwiwa tsakaninsu. Sin ta ba da babbar gudummawa ga harkokin MDD. Kuma Sin za ta ci gaba da shiga a dama da ita tare da nuna goyon baya ga yin hadin gwiwa da MDD a duk fannoni, ta yadda za ta samu nasara a kokarin da ta ke yi na tabbatar da tsari da dokokin kasa da kasa yadda ya kamata.
A nasa bangare, mista Guterres ya nuna godiya ga kasar Sin bisa goyon bayan da ta nuna masa kan nasarar da ya samu ta zama magatakardar MDD. Ya ce, yanzu Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan MDD da ma tsarin kasancewar bangarori daban daban. MDD na fatan karfafa hadin gwiwa tsakaninta da Sin, domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da samar da wadata a duniya.(Fatima)