Eugene Owusu, babban jami'in MDD mai kula da aikin jin kai dake Sudan ta Kudu, ya yi kira a ranar Laraba ga dukkan bangarorin dake gaba da juna a kasar da su ba da wata dama cikin 'yanci, da kariya ga ma'aikatan jin kai.
Mista Owusu, mai kula da harkokin jin kai game da kasar Sudan ta Kudu, ya bayyana babbar damuwa game da tasirin wani jerin shingaye na gwamnati da matsalolin samar da ayyukan jin kai a cikin wannan kasa da yaki ya lallasa.
Kungiyoyin jin kai a Sudan ta Kudu na kakowa ko wace rana domin ceton rayuka, da kuma rage kaifin wahalhalu a cikin kasar. Amma duk da haka suna fuskantar shingaye da matsaloli dake kawo tarnaki ga kokarinsu. Dole a daina, in ji mista Owusu a cikin wata sanarwar da aka fitar a Juba. Bukatun jin kai na kasar na ci gaba da karuwa, dalilin yakin basasa, da kuma faduwar tattalin arziki, in ji jami'in.
Ana kiyasta cewa, kimamin mutane miliyan uku suka kaura, wadanda kuma fiye da miliyan 1,1 suka gudu zuwa kasashe makwabta, tun farkon barkewar yaki tsakanin sojojin shugaba Salva Kiir da dakarun tsohon mataimakinsa Riek Machar da aka sallama a cikin watan Disamban shekarar 2013, lamarin da ya kawo cin zarafi kan ma'aikatan jin kai, kuma wani shisshigi a cikin aikin jin kai. (Maman Ada)