Kwamishinan majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika Smail Chergui, ya ce, kwamitin tsaro na MDD UNSC da majalisar zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar Afrika AU, za su hada gwiwa domin tunkarar shirin maido da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.
Chergui, ya bayyana hakan ne ga 'yan jaridu a Addis Ababa cewa, kwamitin tsaron na MDD ya yi wa wakilan kungiyar tarayyar Afrika karin haske game da ziyarar da ya kai Sudan ta Kudun, da kuma tattaunawar da ya yi da mahukuntan kasar.
A wata takardar bayan taro da aka fitar bayan tattaunawar da kwamitin tsaron MDD ya yi da shugaba Silva Kiir a ranar Lahadi, UNSC ta ce, sun cimma matsaya tsakanin kwamitin MDD da gwamnatin Sudan ta Kudu cewa, za su yi aiki tare a matsayin wata sabuwar yarjejeniyar da za ta kawo karshen tashin hankalin da al'ummar kasar Sudan ta Kudun ke fuskanta, musamman wajen tabbatar da adalci, da 'yancin al'umma, da samun makoma mai kyau a nan gaba ga jama'ar kasar.(Ahmad Fagam)