Tawagar MDD da ake aiki a Sudan ta Kudu ta zargi gwamnatin kasar da hana ma'aikatan bayar da agaji fita daga sansanoninsu da ke Bentiu don gudanar da ayyukansu.
Jami'in kula da harkokin jin kai na MDD da ke Sudan ta Kudu Toby Lanzer ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai, yana mai cewa, mahukuntan Sudan ta Kudu sun hana ma'aikatan gudanar da ayyukansu a Bentiu da kewaye.
Lanzer ya ce, wannan mataki da gwamnatin Sudan ta Kudu ta dauka kan ma'aikatan na MDD ya kawo cikas ga ayyukan ceton rayuka, wadanda suka hada da taimakawa asibitoci. Don haka ya kara yin kira ga sassan da ke fada da juna a kasar da su martaba 'yancin da hukumomin bayar da agajin ke da shi na gudanar da ayyukansu a Sudan ta Kudu.
Sai dai kuma ministan watsa labarai na Sudan ta Kudu Micheal Makuei ya shaidawa Xinhua cewa, sun dauki wannan mataki ne a matsayin kandaganki don tabbatar da tsaro ga ma'aikatan agajin kasa da kasa.
Mahukuntan Sudan ta Kudu na zargin tawagar MDD da ke Sudan ta Kudu da wuce makadi da rawa inda a mafi yawan lokuta suke daukar kansu tankar gwamnatin kasar. (Ibrahim)