Mahukuntan kasar Sudan ta Kudu sun ki amincewa da shawarar janye korar da suka yiwa Toby Lanzer, jami'in MDD mai lura da ayyukan jin kai a kasar.
A jiya Talata ne mahukuntan kasar suka jaddada wannan mataki da suka dauka kan Mr. Lanzer. Hakan kuwa na zuwa ne a gabar da hukumomin kasa da kasa ke ci gaba da kiraye-kirayen dakatar da korar jami'in.
Da yake karin haske game da hakan, kakakin gwamnatin Sudan ta Kudun Ateny Wek, ya ce, majalissar zartaswar kasar ce ta tabbatar da wannan mataki, sakamakon kalaman batanci ga gwamnati da Mr. Lanzer ya yi.
Tuni dai babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya soki wannan mataki, yana mai kira ga mahukuntan kasar da su sake duba matakin, wanda a cewar sa ya sabawa ka'ida.
A shekakar 2011 ne Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai daga kasar Sudan, sai dai jim kadan da hakan, sai aka fara samun tashe-tashen hankula tsakanin sojojin dake biyayya ga gwamnati, da na korarren mataimakin shugaban kasar Riek Machar. (Saminu)