Sin tana goyon bayan kwamitin sulhun MDD da ya kara daukar matakai a nan gaba game da gwajin nukiliyar Koriya ta Arewa
Rahotanni na nuna cewa, kwamitin sulhu na MDD zai zartas da wani sabon kuduri game da kakabawa kasar Koriya ta Arewa takunkumi, wanda zai rage kudin shigar da za ta samu a fannin kwal, adadin da zai kai kimanin dalar Amurka miliyan 400 a ko wace shekara. Baya ga haka, kudurin zai hana kasar ta Koriya ta Arewa fitar da tagulla, Nickel, azurfa da kuma kwano. Game da haka ne, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau a nan birnin Beijing cewa, Sin ba za ta bayyana ra'ayinta kan wannan batu ba saboda har yanzu ba a zartas da wannan kuduri ba tukuna. Amma, a sa'i daya ya jaddada cewa, kasar Sin na goyon bayan kwamitin sulhun MDD da ya ci gaba da daukar matakai a nan gaba kan gwajin nukiliya karo na 5 da Koriya ta Arewa ta yi. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku