Kwamitin sulhu ya kara bayyana bakin cikinsa saboda bambancin da ya kunno kai tsakanin mambobin kwamitin, saboda yanzu haka 'yan kasar Koriya ta Arewa na cikin wani hali, amma gwamnatin kasar ta yi amfani da albarkatun kasar domin kera makamai masu linzami.
A sa'i daya kuma, kwamitin sulhu ya nuna damuwa sosai kan jerin harba makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ta harba, bayan wadanda ta yi a ranar 15 da ranar 23 ga watan Aflilu.
Kwamitin sulhu ya sake nanata cewa, kamata ya yi Koriya ta Arewa ta dakatar da daukar matakan da za su saba wa kudurorin kwamitin sulhu, ciki har da yin gwajin makaman nukiliya, tare kuma da daukar nauyinta bisa kudurorin.
Baya ga haka, kwamitin sulhu ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya, da yankin arewa maso gabashin Asiya, ya kuma bayyana cewa, zai yi kokarin warware matsalolin da ake fuskanta a yanzu a siyasance ta hanyar lumana da diplomasiya, kana yana maraba da kasashe mambobinsa da sauran kasashe da su bullo da wani shirin warware matsaloli cikin lumana a dukkan fannoni.
Kwamitin sulhun kuma zai ci gaba da lura da halin da yankin ke ciki, kuma mai yiwuwa ne zai dauki matakai masu tsanani idan bukatar hakan ta taso. (Bilkisu)