Kwamitin sulhun ya kuma bukaci sauran mambobin kwamitinsa da su cimma matsaya guda, wajen warware wannan kalubale cikin lumana kuma daga duk fannoni. Kwamitin sulhu na M.D.D. ya ce, zai ci gaba da la'akari da yanayin da ake ciki a kasar, tare da daukar karin matakai.
A daya hannun ita ma gwamnatin Koriya ta Kudu ta yi Allah-wadai da matakin da Koriya ta Arewa ta dauka na harba makamai masu linzami, kuma a cewarta, za ta yi hadin gwiwa da kasashen duniya, don daukar matakai na hakika.
Koriya ta Arewa dai ta gudanar da taron kwamitin tsakiyar kasar, don bikin murnar cika shekaru 84 da kafa sojojin jama'ar Koriya ta Arewa. A yayin taron ne kuma babban hafsan-hafsoshin sojojin jama'ar Koriya ta Arewa Ri Myong Su, ya yi kashedi ga kasashen Koriya ta Kudu da Amurka da kada su kalubalanci shugaban kasar sa.(Bako)