in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta Arewa ta sake kasa cimma nasarar harbar makamai masu linzami
2016-04-29 10:39:28 cri
Kamfanin dillancin labaru na kasar Koriya ta Kudu, ya ruwaito rundunar sojan kasar na cewa Koriya ta Arewa ta gaza, a yunkurin ta na harba makamai masu linzami samfurin "Musudan" mai cin matsagaicin zango ko IRBM a takaice.

Bisa rahotanni daga rundunar sojin kasar Koriya ta Kudu, an ce, a jiya Alhamis da karfe 6 da minti 40, Koriya ta Arewa ta harbi wani abu da ya yi kama da makami samfurin IRBM, amma nan take ya fado bayan da aka harba shi.

A ranar 15 ga wannan watan nan, rundunar sojin kasar Koriya ta Kudu ya bayyana cewa, Koriya ta Arewa ta harba makamin IRBM a karo na farko a yankin gabashin gabar teku dake zirin Koriya, sai dai gwajin makamin bai yi nasara ba.

Ana amfani da hanyar harbar makamin IRBM ne ta roka, kuma makamin na cin tsakanin kilomita 3000 zuwa 4000, don haka zai iya kaiwa ga dukkanin yankunan Koriya ta Kudu, da Japan, da sansanin soja na Amurka dake tsibirin Guam a yammacin tekun Pasific.

A jiya ne kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, ana nuna damuwa bisa ga yadda Koriya ta Arewa take sake gwajin harbar makamai masu linzami, inda MDD ya kalubalanci Koriya ta Arewa da ta dakatar da duk wane mataki na tsokana, ta kuma yi biyayya ga ka'idojin kasa da kasa.

Kwamitin sulhun MDD ya canja ajandar sa jiya, inda ya tsaida kudurin gudanar da shawarwari cikin sirri kan batun Koriya ta Arewa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China