Shugaban kasar Sin ya yi kiran a dauki matakan ceton wadanda suka ji rauni a wani kamfanin samar da wutar lantarki
Da misalin karfe 8 sauran minti 20 na safiyar yau Alhamis agogon kasar Sin ne, aka samu wani mummunan hadarin rugujewar dandalin gina tankin sanyaya na'ura a wani kamfanin samar da wutar lantarki na Fengcheng a lardin Jiangxi dake kudancin kasar Sin. Ya zuwa karfe 6 da rabi na maraice, mutane 67 sun mutu, kana wasu mutane 2 kuma suka ji raunuka.
Bayan da ya samu wannan mummunan labari, ba tare da bata lokaci ba, Mr. Xi Jinping, shugaban kasar Sin wanda yake ziyara a Latin Amurka ya ba da umurni, inda ya bukaci gwamnatin lardin Jiangxi da hukumomin da abin ya shafa da su yi kokarin daukar matakan ceto da kwantar da hankulan iyalan mutanen da suka mutu sanadiyar hadari. Bugu da kari, ya bukace su da su hanzarta gudanar da bincike don gano musabbin hadarin. (Sanusi Chen)