A jiya Talata ne aka bude taron kolin kafofin watsa labaru na Sin da Latin Amurka a San Diego, hedkwatar kwamitin kula da harkokin tattalin arzikin kasashen Latin Amurka da Caribbean ta MDD.
A yayin bikin, shugaban gidan rediyon kasar Sin wato CRI mista Wang Gengnian, ya gabatar da jawabi, inda ya yi kira ga kafofin watsa labaru na Sin da Latin Amurka da su fadada fannonin da za su hada kai, tare kuma da daga matsayi da inganci wajen hadin kansu, da nufin taimaka wa bangarorin biyu wajen zurfafa hadin kai.
Shugabanni da wakilai da suka fito daga kafofin watsa labaru fiye da 80 na kasashen Latin Amurka sama da 20 ne, da kuma manyan jami'ai da suka fito daga muhimman kafofin watsa labaru kimanin 20 na kasar Sin suka halarci wannan taron kolin. (Bilkisu)