Jiya 22 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron koli na kafofin watsa labaru na Sin da Latin Amurka bisa rakiyar takwararsa ta kasar Chile Michelle Bachelet, wanda aka shirya a San Diego, hedkwatar kwamitin kula da harkokin tattalin arzikin kasashen Latin Amurka da Caribbean ta MDD.
A yayin bikin, shugaba Xi ya gabatar da jawabi mai taken bude sabon babin hadin kai tsakanin kafofin watsa labaru na Sin da kasashen Latin Amurka.
A jawabinsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, shirya taron kolin kafofin watsa labarun wani muhimmin aiki ne, saboda yin cudanya a tsakanin Sin da Latin Amurka ya kasance wani muhimmin batu game da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, kuma kafofin watsa labaru suna taka muhimmiyar rawa wajen dada inganta zumunci a tsakanin jama'ar Sin da Latin Amurka. (Bilkisu)