A jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da takwararsa ta kasar Chile Verónica Michelle Bachelet Jeria, a birnin San Diego, inda shugabannin biyu suka nuna yabo sosai kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashensu, kana suka tsaida kuduri game da daga matsayin dangantakarsu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da nufin ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.
Bayan shawarwarin kuma, shugabannin biyu sun sa ido kan yadda ake sa hannu kan wasu takardun hadin kai a tsakanin bangarorin biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, aikin gona, binciken ingancin kaya, al'adu, ba da ilmi, ciniki ta yanar gizo, aikin sadarwa da kuma sha'anin kudi da dai sauransu. (Bilkisu)