Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi jawabi mai taken "hadin kan juna tare da samar da kyakkyawar makomar dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka" a majalisar dokokin kasar Peru a yammacin ranar 21 ga wannan wata inda ya jaddada cewa, kamata ya yi bangarorin biyu su bi manufar samun bunkasuwa cikin lumana da hadin gwiwa da juna, da yin kokarin raya bangarorin biyu tare, da cimma burinsu ta hanyar yin hadin gwiwa, da sa kaimi ga inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu a dukkan fannoni zuwa wani sabon matsayi.
Xi Jinping ya bada shawarwari guda hudu, na farko, a yi hadin gwiwa da samun bunkasuwa cikin lumana, da yin kokarin raya bangarorin biyu yadda ya kamata. Na biyu, a sa kaimin aiwatar da manufofin samun bunkasuwa tare. Na uku, a inganta hadin gwiwarsu don samun wadata a bangarorin biyu. Na hudu, a more nasarorin hadin gwiwarsu domin amfanawa jama'arsu.
Haka zalika, shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da bin hanyar samun bunkasuwa tare, da aiwatar da manufar samun moriyar juna, kuma tana maraba da kasa da kasa da su more ci gaban da kasar Sin ta samu da cimma burin samun bunkasuwa tare. Sin tana da kyakkyawar makomar bunkasuwar tattalin arziki, wadda za ta samar da gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya. Sin tana son yin kokarin tare da bangarori daban daban don sa kaimi ga samun bunkasuwa mai daidaita da karfi a fannin tattalin arzikin duniya. (Zainab)