in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da Barack Obama
2016-11-20 13:11:05 cri
A ran 19 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda a halin yanzu yake halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik watau APEC karo na 24 da ake yi a kasar Peru, ya gana da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama a babban birnin kasar, Lima.

A yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya yaba wa shugaba Obama kan babbar gudummawar da ya bayar domin raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka.

Haka kuma, Xi Jinping yana fatan kasashen biyu za su ci gaba da yin hadin gwiwa domin tabbatar da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin yanayin zaman karko, a lokacin da ake sauyin mulki a kasar ta Amurka, ta yadda za a bude wani sabon shafin dangantaka a tsakanin Sin da Amurka. Haka kuma, kasar Sin tana sa ran karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Amurka, har ma da dukkan sassa masu halartar taron, domin ciyar da taron da ake yi a kasar Peru gaba, ta yadda za a inganta hadin gwiwar tattalin arziki a yankin, yayin da ake samar da damammaki masu kyau ga bunkasuwar tattalin arziki a kasashen dake yankin na Asiya da Pasifik.

Ganawa ta wannan karo ita ce ta farko da shugaba Xi da shugaba Obama suka yi a tsakaninsu bayan babban zaben sabon shugaban kasar Amurka, kuma ta kasance ganawa ta karshe tsakanin shugabannin biyu.

A yayin ganawar tasu, shugaba Obama ya bayyana cewa, babu shakka, bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka za ta tallafa wa al'ummomin kasashen biyu, har ma ga kasa da kasa baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China