A yayin shawarwarin, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, shekaru biyar masu zuwa zai zama muhimmin wa'adi na bunkasa Sin da Peru. Kasar Sin za ta kammala burin farko dake cikin "Buruka biyu na tsawon shekaru 100", yayin da Peru za ta cimma nasarar zamanintar da kanta. A cikin sabon yanayi kuma, kamata ya yi mu dora muhimmanci kan tsara wani jadawali a matsayin koli da sa kaimi ga gudanar da shi, da yin amfani da tsarin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, domin aiwatar da shirin aikin kasashen biyu daga shekarar 2016 zuwa ta 2021.
A nasa bangare, shugaba Kuczynski ya bayyana cewa, yanzu ana ci gaba da raya dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban bisa manyan tsare tsare, akwai makoma mai kyau wajen hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya da kuma al'adu a tsakaninsu. Peru na fatan daga matsayin yarjejeniyar yankin cinikayya cikin 'yanci tare da kasar Sin, kuma tana marhabin da kamfanonin kasar Sin wajen kara zuba jari ga sha'anin ma'adinai, da makamashi, da samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa, da sufuri, da manyan kayayyakin amfanin jama'a da sauransu na kasar. Tana kuma fatan karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tarbiya da al'adu da kuma yawon shakatawa, domin kara yin mu'amala tsakanin jama'ar kasashen biyu.(Fatima)