Wadannan ma'aikata za su fuskanci zargin da za a gabatarwa kotu da ya hada da laifin kisan kai, yunkurin kisan kai, da kuma gazawarsu wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata da dai sauransu.
Haka zalika, za a gabatar wa kotun alhakin rasa rai, ko jikkata sakamakon rashin kulawa, da kuma keta dokar aikin ceto a hadarin na teku ga sauran ma'aikata guda goma sha daya.
Jirgin ruwan fasinjan dai mai dauke da mutane 476 ya nutse ne a ruwan Koriya ta Kudu ranar 16 ga watan da ya gabata, inda aka samu nasarar ceto mutane 172 daga cikin fasinjojin, kuma ya zuwa yanzu akwai mutane 20 da ba kai ga sanin inda suke ba. (Maryam)