A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana kuma, hukumar 'yan sandan teku na Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, ana cigaba da aiki karkashin ruwa bi da bi ba tare da kasala ba, domin lalube mutanen da suka lake cikin wannan jirgin ruwa. A safiyar yau, an samu ganin gawawwaki uku masu sanye da rigar ceto cikin jirgin, saidai kuma mawuyacin yanayi na kawo cikas wajen ci gaba da aikin ceto da na debo gawawwaki. Tun rana ta farko, masu aikin ceto suke kokarin aika sakwanni zuwa cikin jirgin ruwan, amma har zuwa yanzu, ba a samu martani ko kadan ba.(fatima)