Wakilin kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana jiya Laraba cewa, kasar Sin tana fatan kasashen Amurka da Cuba za su cigaba da shimfida yunkurin raya huldar dake tsakaninsu yadda ya kamata, kuma Amurkar ta hanzarta dage takunkumin da ta kakabawa Cuba daga dukkan fannoni, wanda ya dace da cin moriyar bai daya ta kasashen dama jama'ar kasashen biyu. Wannan mataki zai taimaka wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk nahiyar Amurka, tare da ci gaban al'ummar duniya baki daya.
A shekarar 1962 ne, shugaban Amurka na wancan lokaci John F. Kennedy, ya ba da umurni sanya wa Cuba takunkumi a fannonin tattalin arziki, da sha'anin kudi, da kuma cinikayya.(Kande Gao)