A jiya Laraba ne, a yayin babban taron MDD karo na 71 aka zartas da wani kuduri da babban rinjaye, inda aka sake kalubalantar kasar Amurka da ta janye takunkumin fiye da shekaru 50 da ta sanyawa kasar Cuba a fannonin tattalin arziki da cinikayya da kuma sha'anin kudi.
Wannan shi ne karo na farko da Amurka ta jefa kuri'ar janyewa a maimakon nuna adawa. Dukkan mambobin MDD 193 sun jefa kuri'unsu game da wannan kuduri, inda a karshe aka samu kasashe 191 da ke goyon bayan kudurin, sai kuri'un kasashen biyu wato Amurka da Isra'ila da suka janye daga kudurin. Tuni babban taron MDD ya zartas da kudurin da abin ya shafa har zuwa shekaru 25 a jere.(Kande Gao)