An zartas da kudurin a gun babban taron MDD a wannan rana, inda aka kara kalubalantar kasar Amurka da ta soke kangiyar da ta yiwa kasar Cuba a fannonin tattalin arziki da cinikayya da hada-hadar kudi. Wannan ne karo na 24 a jere da babban taron MDD ya zartas da kuduri kamar haka.
Liu Jieyi ya yi jawabi kafin jefa kuri'u cewa, Amurka ba ta dakatar da kangiyar da ta yiwa kasar Cuba a fannonin tattalin arziki da kasuwanci da hada-hadar kudi ba, wannan ya sabawa ka'idojin tsarin mulkin MDD da kudurorin da babban taron MDD ya zartas, kuma ya kawo hasarori ga kasar Cuba a fannin tattalin arziki, da kawo cikas ga jama'ar kasar Cuba wajen kawar da talauci, da yunkurinsu na sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma cimma burin bunkasuwa na shekarar 2000, kana ya taka ikon yin rayuwa da samun bunkasuwa na jama'ar kasar Cuba, da kuma kawo illa ga yin mu'amala a tsakanin Cuba da sauran kassahen duniya a fannonin tattalin arziki da kasuwanci da hada-hadar kudi.
Hakazalika kuma, Liu Jieyi ya ce, Sin tana girmama ikon kasa da kasa na zabar tsarinsu da hanyoyin samun bunkasuwarsu, da kuma yin watsi da saka takunkumi ga wata kasa ta hanyar aikin soja ko siyasa ko tattalin arziki da dai sauransu. (Zainab)