A ranar litinin ne, shugabannin kasashen Amurka da Cuba bi da bi suka yi jawabi a gun muhawarar babban taron MDD. A jawabin sa Shugaba Obama ya nuna imanin da cewa, majalisar dokokin kasar Amurka za ta soke manufar hana yin jigilar kaya zuwa ga kasar Cuba. Shi kuma a nashi jawabin Shugaban na Cuba Raul Castro kira ya yi ga kasar Amurka da ta soke takunkumin da ta sanya ma kasarsa a fannonin tattalin aziki, cinikayya da hada-hadar kudi. Haka kuma ya bukaci kasar Amurka da ta mayar da yankin Guantanamo da samar da diyya ga jama'ar kasar Cuba wadanda suka samu hasarori da dama a shekaru fiye da 10 da suka wuce. (Zainab)