Hukumar daidaita ma'aikatun aikewa da sakwanni da sadarwar fasahohin zamani (ARPCE) ta yi alkawari na kawo tallafin kudin shekara shekara na fiye da kudin Sefa miliyan 500 a ranar Asabar a Brazzavile na kasar Congo domin aiwatar da shirin Yekolab da ya kasance wata muhimmiyar cibiyar da za ta rika samarwa matasa horo kyauta kan ayyukan fasahar zamani.
Muna zuba kudi ga mutanen da za su kawo sauyi ga dumiyarmu ta gobe. Abu ne mai kyau sosai na ganin cewa, mun zuba kokari domin samun sakamako mai kyau, in ji darekta janar na hukumar daidaita ma'aikewa da sakwanni da sadarwar fasahohin zamani (ARPCE), Yves Castanou, a gaban 'yan jarida, tare da yin kira ga sauran kamfanoni na cikin gida da su koyi da irin wannan shiri. (Maman Ada)