Babban sakataren kwamitin kasar Sin mai kula da dandalin hadin kan Sin da Afrika (FOCAC) Lin Songtian, ya fada a Litinin din nan cewar, kasar Sin za ta tallafawa jamhuriyar dimokaradiyyar Congo wajen aiwatar da shirinta na musamman na ci gaban tattalin arziki wato SEZ a takaice.
Lin, ya furta hakan ne a Brazzaville, babban birnin jamhuriyar demokaradiyyar Congo a lokacin ziyarar aiki a kasashen Afrika.
Bayan ganawa da jami'an Congo, jami'in kasar Sin ya bayyana cewar, wasu muhimman batutuwa biyu ne suka sa ziyarar tasa zuwa kasar.
Dalili na farko shi ne, domin karfafa yarjejeniyar da aka kulla a lokacin ziyarar shugabannin kasashen biyu, wato ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai Congon a watan Maris na shekarar 2013, da kuma ziyarar shugaba Denis Sassou N'Guesso na kasar zuwa Sin a watan Yunin shekarar 2014. Batu na biyu shi ne, karfafa ci gaban da aka samu a taron FOCAC, wanda aka kammala a kwanan nan a birnin Johannesburg na Afrika ta kudu.
Gwamnatin Congo ta shirya kafa wasu cibiyoyin 4 na musamman na bunkasa ci gaban tattalin arziki tun a shekarar 2013 a Brazzaville, da Pointe Noire, da Ouesso da kuma Oyo-Ollombo, ta hanyar amfani da kwarewar da ta samu daga kasar Sin.
Congo ta bullo da wadannan shirye shiryen ne, domin kawo karshen dogaro kan man fetur don samar da ayyukan yi, da sarrafa kayayyaki a masana'antu, da kuma kawar da talauci.
An kulla dangantaka tsakanin Sin da jamhuriyar demokaradiyyar Congo ne tun a shekarar 1964. Kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta shafi bangarorin samar da kayayyakin more rayuwa da kare muhalli, da kiwon lafiya, da wasanni da kuma raya al'adu.(Ahmad Fagam)