in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Raba gardama kan kundin tsarin mulkin Congo ya gudana cikin kwanciyar hankali
2015-10-26 10:43:34 cri

Raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki da shugaban kasar Congo Denis Sassou N'Guesso ya kira ya gudana a ranar Lahadi kamar yadda aka tsara a dukkan fadin kasar cikin kwanciyar hankali, ba tare da kwararar mutane a safiyar wannan rana ba, a cewar wasu mazauna birnin Brazzaville.

Ko da yake, an fara zaben da masalin karfe bakwai na safe, amma wasu rumfunan zaben sun fara karbar masu zabe wajen karfe tara na safe.

Bayan kamfen 'yan adawa na nuna adawa da gyaren fuska kan kundin tsarin mulki da ya janyo tashe tashen hankali, zaben ranar Lahadi ya gudana cikin matakan tsaro na 'yan sanda a wasu unguwannin dake kudancin Brazzaville, musammun ma da suka fi fama da zanga zanga a farkon mako.

Bayan fargabar da wadannan tashe tashen hankali suka janyo a cikin muhimman biranen Brazzaville da Pointe-Noire, halartar zaben ta zama wani babban mataki na wannan zaben raba gardama.

Yau rana ce mai muhimmanci ga al'ummar kasar Congo, domin za su nuna wa duniya cewa, su al'umma ce mai 'yanci da walwala. Idan an ce batutuwa ne da suka shafi rayuwar mutane da makomarsu, to 'yan kasa suna yin zaben domin tabbatar da burinsu ne, ba wai domin wani daban ba, in ji shugaban kasar Denis Sassou N'Guesso a ranar Lahadi da safe bayan ya kada kuri'arsa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China