Bayan manyan ayyukan da aka gudanar cikin watanni goma sha biyu da suka gabata, kamfanin gina hanya da gada na kasar Sin CRBC ya mika wa gwamnatin Congo babbar gadar da ta hada Brazzaville da Kintele, wanda ta ratsa ruwan tafkin Congo, bisa tsawon kilomita 6,8.
Shugaban kasar Congo Denis Sassou N'Guesso ya kaddamar da bikin bude wannan gadar da aikin gina ta ya lakume Sefa fiye da biliyan 106 kwatankwacin dalar Amurka fiye da miliyan 170.(Maman Ada)