Dakarun sojin gwamnatin kasar Somalia (SNA), wadanda ke samun goyon bayan dakarun wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika (AMISOM), ta samu nasarar kwace wasu yankuna 4 a kusa da garin Bardhere dake kudancin lardin Gedo a kasar Somalia daga hannun mayakan Al-Shabaab.
Kwamandan sojojin gwamnatin Somalia dake yankin Osman Sheikh, ya fada wa 'yan jaridu a Mogadishu cewa, manufar kaddamar da sintiri da jami'an ke gudanarwa ita ce, domin kwato muhimman yankunan kasar wadanda mayakan 'yan ta'adda ke fakewa don kaddamar da hare-hare.
Runduna ta 9 ta dakarun sojoji na SNA, sun gudanar da sintirin a yankunan Matano, da Anole, da Tubako da Qutaley, domin farautar mayakan 'yan ta'addan a yankunan wadanda ke da tazarar kilomita 30 da garin Bardhere.
Osman ya kara da cewa, a halin yanzu, dakarun kasar na rike da ikon yankunan 4, sai dai mayakan 'yan ta'addan sun tsere a lokacin da suka kai samammen, amma ya ba da tabbatacin ci gaban da farautarsu.
Mayakan na Al-Shabaab sun sha kaddamar da hare-hare a gefen tituna kan dakarun na AU da jami'an gwamnatin Somalia. (Ahmad)