Cikin sanarwar, an yi bayani kan ayyukan da tawagar kwararrun za ta aiwatar, wadanda suka kunshi sa ido kan yadda ake gudanar da zaben da ba na kai tsaye ba a Somalia a shekarar 2016, gami da rike shi yadda ya kamata. Haka kuma za su share fage ga wani shirin siyasa da aka tsara na ganin kowane dan kasar Somaliya ya jefa kuri'arsa guda zuwa shekarar 2020.
Sauran ayyukan da kwararrun kungiyar AU za su gudanar sun hada da hadin gwiwa tare da MDD, da kungiyar tarayyar kasashen Turai EU, da kungiyar kasashen Larabawa, don tabbatar da gudanar babban zaben a kasar Somalia lami lafiya, ba tare da gamuwa da matsala ba. Sa'an nan, an ce tawagar kwararrun za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 5 ga watan Nuwamban bana.(Bello Wang)