Jami'an gwamnatin Jubba sun bada tabbacin garin ya fita daga hannun mayakan Raskamboni. Garin Kudhawanda ke gabar ruwa kusa da kan iyakar Somalia da kasar Kenya yana da mahiummanci ga kungiyar Al-shabab musamman saboda amfanin da take da garin a matsayin tashar ruwa.
Tun farko mayakan Raskamboni, masu biyayya ga gwamnatin Jubba, su ne suka fara kwace garin daga hannnun Al-shabab, makonni biyu da suka wuce.
Kakakin gwamnatin Jubba, Yusuf Mohammed ya bada tabbacin cewar mayakan Al-shabab sun kaddamar da wani gagarumin farmaki a ranar Asabar, inda suka kwace garin na Kudha.
Hussein yace duk da cewa dakarunsa sun janye daga garin saboda dabarun yaki, to amma sojojin zasu koma, kuma za'a ci gaba da aranagama da juna in dai har 'yan kungiyar ta Al-shabab suka ci gaba da kasancewa a yankin.,
A kuma bangare guda kakakin sojoji na kungiyar Al-shabab sheikh Abdulaziz Abu Musa yayi ikirarain cewar, mayakansa sun kashe sojojin gwamnatiun Jubba 63, kamin su kwace iko a garin Kudha.
A kuma daya bangare, jama'ar gari sun bayar da tabbaci cewar dukanin bangarorin biyu, da kuma farar hula, sun yi asarar rayuka a lokacin da akayi bata kashin wanda ya dauki awowi 4 ana fafatawa.(suwaiba)