in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Somaliya da sojojin AU sun karbe wani birni daga hannun mayakan Al-Shebab
2014-10-05 16:55:50 cri

Sojojin gwamnatin kasar Somaliya tare da taimakon sojojin wanzar da zaman lafiya na tarayyar Afrika (AU) sun sanar a ranar Asabar da karbe wani birnin dake bakin ruwa dake tsakiyar kasar daga hannun mayakan Al-Shebab, in ji kafofin watsa labarai da kuma jami'an kasar.

Rundunar sojojin kasar Somaliya (SNA) tare da taimakon sojojin wanzar da zaman lafiya na AMISOM, ta karbe birnin dake bakin ruwa na Adale dake yankin Moyen-Shabelle, bayan mayakan kungiyar Al-Shebab sun ari ta kare, in ji wata sanarwar tawagar AU dake kasar Somaliya da ake kira AMISOM.

A cewar kafofin watsa labarun kasar, birnin Adale, muhimmiyar cibiyar kasuwanci ce ta yankin Moyen-Shabelle, mai tazarar kilomita 220 a arewa maso gabashin birnin Mogadishu, an karbe ba tare da wani gumurzu ba, mayakan Al-Shebab sun ari ta kare a yayin da suka ga dakarun kawance sun kusanto su.

Kungiyar Al-Shebab, dake alaka da Al-Qaida, na samun ja-da-baya a lokacin baya-bayan nan, bayan an kore ta daga yawancin biranen da ta mamaye a kudanci da tsakiyar kasar. Ci-gaban da aka samu ya zo daidai da sojojin gwamnatin Somaliya tare da taimakon sojojin AMISOM suka kaddamar a cikin watan Satumba da wani babban samame domin fadada ikonsu a yankunan dake hannun mayakan kishin islama na Al-Shebab. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China