Wannan mataki ya biyo bayan wani zaman taron da aka yi a Juba a karkashin jagorancin janar Alfred Lado Gore, dake kwamandan na biyu a cikin wannan kungiya ta tsoffin 'yan tawaye, bisa burin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba wa hannu a cikin watan Augustan shekarar 2015.
Bisa rashin halartar mataimakin shugaban kasa Riek Machar na dan lokaci, shugabannin adawa a Juba sun nada Taban Deng Gai da ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko, in ji Ezecheil Luol Gatkuoth, mai kula da harkokin cikin gida na SPLM-IO a gaban 'yan jarida.
Ya kara da cewa, mista Gai yayi alkawarin cewa zai janye daga sabon matsayinsa idan mista machar da ya tsere daga Juba bayan barkewar rikici, ya dawo Juban domin kama aikinsa.
A nasa bangare, mista Gai ya bayyana cewa nadinsa a matsayin mataimakin shugaban kasa na rikon kwarya a cikin gwamnatin hadaka na da manufar cike wannan kujera da ba kowa kamar yadda yarjejeniyar ta tanada da kuma cigaba da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.
Yana tabbatar wa masu goyon bayansa da cewa, bayan da ya halarci yakin kwato 'yancin wannan kasa, zai yi iyakacin kokari domin hana dawowar yaki, in ji mista Gai.
Haka kuma, yayi kira ga mambobin na bangaren tsoffin 'yan tawaye da su dawo aiki tare da shi domin ciwo kan Riek Machar da ya dawo Juba. Zai yi murabus da baiwa Machar damar koma wa matsayinsa idan ya dawo, in ji mista Gai.
Ya kasance mai rike amana ga dukkan shugabanni tun a shekarar 1983 a lokacin yakin neman 'yanci wanda ya kai ga samun 'yancin kan Sudan ta Kudu a shekarar 2011. (Maman Ada)