in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki Moon ya bukaci a dauki matakan bai daya game da Sudan ta Kudu
2016-07-18 20:09:37 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, ya bukaci daukacin sassan masu ruwa da tsaki a rikicin Sudan ta Kudu, da su dauki matakan bai daya, don ganin an cimma nasarar warware rikicin dake addabar kasar.

Mr. Ban ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi gaban taron wakilan kungiyar shugabannin kasashen Gabashin Afirka ta IGAD, wanda ya gudana a birnin Kigali.

Yayin taron wanda ya zo daidai lokacin da kungiyar hadin kan Afirka ta AU ke gudanar da nata taron, Ban Ki Moon ya ce, lokaci ya yi da za a hada karfi da karfe, wajen zakulo bakin zaren wannan matsala. Ya kuma yi maraba da matakin da majalissar tsaro da wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU da hadin gwiwar IGAD suka dauka, na yin Allah wadai da barkewar tashin hankali a Sudan ta Kudu.

Ban Ki Moon ya kuma nanata kira ga mahukuntan kasar da su kaucewa matakan da ka iya rura wutar rikici.

IGAD dai na goyon bayan matakai uku da Ban Ki Moon ya gabatar, game da warware takaddamar da ta dabaibaye Sudan ta Kudun, matakan dai su ne kakaba takunkumin shigar da makamai cikin kasar, da kara sanyawa shuwagabannin kasar dake yi wa zaman lafiya kafar ungulu takunkumi, tare da karfafa ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD mai aiki a kasar ko UNMISS a takaice.

Mahalarta taron dai sun kunshi shugabannin kasashen Sudan, da Somaliya, da Uganda da Chadi da Rwanda. Sauran sun hada da shugaba Jacob Zuma na Afirka ta kudu, da fitaministan kasar Habasha wanda shi ne ke jagorantar kungiyar ta IGAD.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China