in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyya mai mulkin Afrika ta Kudu ta bullo da dabarun maido da farin jininta
2016-08-15 10:54:01 cri

Jamiyyar ANC mai mulkin Afrika ta Kudu ta fitar da wasu tsare tsare 14 wadanda za ta yi amfani da su domin shawo kan matsalar raguwar magoya bayanta.

Babban sakataren jam'iyyar ta ANC Gwede Mantashe, ya fada bayan kammala taron kwamitin zartaswa na jam'iyyar wato NEC wanda ya gudana a Pretoria a ranakun 11 zuwa 14 ga wannan wata, biyowa bayan sakamakon zaben kananan hukumomin kasar, inda ya bayyana cewa, ya zama wajibi su dukufa don shawo kan matsalar, kuma dole ne za su bincike yadda ake tafiyar da harkokin jam'iyyar a halin yanzu, musamman wajen nazartar yadda shugabancin jam'iyyar ke gudana daga dukkannin matakai.

Ya ce, za su aiwatar da shirye shirye 14 ba tare da bata lokaci ba don farfado da jam'iyyar ta ANC.

Mantashe ya ce mataki na farko shi ne, kwamitin zartaswa na jamiyyar zai ziyarci dukkanin gundumomin kasar domin ganawa da masu ruwa da tsaki a harkokin jam'iyyar ta ANC da kuma sauraren koke-koken jama'a tare da daukar matakan da suka dace.

Ya ce NEC zai binciki hanyoyin da aka zabo 'yan takarkari, domin gano ko an kakabawa jama'a 'yan takarkarin da su ne suke so ko a'a ba.

Ya kara da cewa, jam'iyyar za ta horas da majalisar kansilolinta domin tabbatar da ganin suna aiwatar da abubuwan da jama'arsu ke bukata.

Da yake maida martini game da batun bada ilmi a kasar kyauta, Mantashe ya fada cewar, NEC zai gana da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ilmi a kasar domin cimma matsaya daya game da kudaden da ya dace a biya daidai da tattalin arzikin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China