in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da dandalin Diplomasiyya tsakanin al'ummar Sin da Afrika a Tanzaniya
2016-08-08 09:48:27 cri

Za a kira taron dandalin diplomasiyya tsakanin al'ummar Sin da Afrika a ran 9 ga wata a birnin Dares Salaam cibiyar tattalin arzikin kasar Tanzaniya, bisa hadin gwiwar kungiya mai kula da harkokin diplomasiyya tsakanin al'ummar Sin da kasashen waje, da kuma gidan rediyon kasar Sin.

A yayin taron, dubban mashahuran masana a fannin siyasa da tattalin arziki na Sin da Afrika, da kuma masana a fannin al'adu da yada labarai, za su yi tattaunawa bisa jigon "Hadin gwiwa da cin moriyar juna, samun bunkasuwa tare da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni tsakanin bangarorin biyu."

Dandalin na da zummar tabbatar da matsaya daya da aka samu a taron koli na Johnnersburg na Afrika ta kudu, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika wato FOCAC, da kuma habaka hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, ta yadda za a aza tubali na samun goyon baya daga jama'a, domin ciyar da dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni tsakanin Sin da Afirka gaba.

Wannan dandali dai ya kunshi sassa uku, ciki hadda karamin dandali na musanyar ra'ayi kan al'adu da yada labarai, da karamin dandali na tuntubar juna da hadin gwiwa kan ayyukan jin dadin jama'a, da karamin dandali na hadin gwiwa ta fuskar kiwon lafiya da magungunan gargajiya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China