James Morgan, wakilin kasar Sudan ta Kudu a kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU, ya ce kasarsa ta nuna juyayi ga mutuwa da kuma jikkatar wasu sojojin kasar Sin da ke aikin kiyaye zaman lafiya yayin dauki-ba-dadin da ya abku tsakanin dakarun bangarorin kasar Sudan ta Kudu a kwanakin baya. Yana kuma fatan ganin kasar Sin za ta ci gaba da baiwa kasar Sudan ta Kudu goyon baya a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.
Morgan ya bayyana hakan ne ga manema labaru yayin da yake halartar taron shugabannin kungiyar AU a birnin Kigali na Ruwanda a ranar Lahadi. Haka zalika ya isar da sakon jajen da shugaban kasarsa Salva Kiir ya nuna wa gwamnatin kasar Sin da jama'arta, musamman ma sojojin da suka ji raunuka, da iyalan sojojin da suka rasu.
A cewar jami'in, kasar Sin babbar aminiyar kasar Sudan ta Kudu ce, wadda ta taka rawar gani a kokarin taimakawa kasar Sudan ta Kudu a fannonin kiyaye zaman lafiya, da samun ci gaban tattalin arziki. A yayin da kasar ke fama da yakin basasa tsakanin shekarun 2013 da 2015, kasar Sin ta yi ta kokarin shiga tsakani don neman samun kwanciyar hankali a kasar. Saboda haka jami'in ya ce yana fatan ganin kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa a kokarin da kasar Sudan ta Kudu ta ke yi na neman zaman lafiya da farfado da tattalin arzikinta.
Ban da wannan kuma, a jiyan ne kuma aka yi bikin zaman makoki a gidan jakadancin kasar Sin dake kasar Uganda, don tunawa da sojojin kasar masu aikin wanzar da zaman lafiya 2 wato Li Lei, da Yang Shupeng, wadanda suka rasa rayuka sakamakon wani harin da aka kaiwa sansaninsu da ke Sudan ta Kudu, a ranar 10 ga wata.(Bello Wang)