Mai rikon mukamin babban hafsan hafsoshin tawagar ta AMISON Kanar Shadrack Othieno Mutacho ya ce kamata ya yi sojojin da ke fafatawa da mayakan na Al-Shabaab su dauki matakan da suka dace tare da kare lafiyar fararen hula.
Mutacho wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da tawagar ta rabawa manema labarai, ya ce, wajibi ne sojojin su kasance masu martaba doka. Bugu da kari, dole ne a kare mata da yara kasancewarsu wadanda suka fi wahala a lokacin rikici.
Kalaman jami'in na zuwa ne bayan da sojojin kungiyar tarayyar Afirka suka halaka wasu fararen hula 4 bisa kuskure, a lokacin da suka kaddamar da wani hari a cikin watan Afrilu kan mayakan Al-Shabaab a Bula Marer da ke yankin Lower Shabelle.(Ibrahim)