Shugabanni da kusoshi da wakilan musamman daga kasashen duniya sama da 10, da ma wakilan wasu kungiyoyin duniya sun halarci wannan biki.
A cikin jawabinsa na kama aiki, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya yi kira ga duk jama'ar kasar da su hada kansu, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar kasar, da cimma burin bunkasa kasar Equatorial Guinea zuwa wani sabon mataki a shekarar 2020, wato zama kasar mai karfin raya tattalin arziki a duniya a lokacin.
Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya kara da cewa, kamata ya yi a bunkasa tattalin arzikin kasar a fannoni da yawa, a bunkasa aikin gona, kiwon dabbobi, da yawon shakatawa da sauransu. A sa'i daya, ya bayyana cewa, kasar za ta dora muhimmanci kan yin hadin gwiwa da sauran kasashen Afirka, da zummar kawar da talauci da yaki da ta'addanci.
A babban zaben da aka gudanar a ranar 24 ga watan Afrulun bana, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya lashe bisa samun kuri'u kashi 93.7 cikin dari da aka jefa. Kuma zai jagoranci wannan kasa bisa wa'adin mulki na shekaru 7 masu zuwa.(Fatima)