in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya rage hasashen karuwar tattalin arzikin duniya na bana
2016-06-08 14:19:21 cri
Bankin duniya ya fidda wani rahoto dake hasashen yanayin tattalin arzikin duniya a ranar Talata, wanda ya bayyana cewa, daga watan Janairun bana, tattalin arzikin duniya ya kara fuskantar matsaloli, kana ana ci gaba da ganin matukar alamun koma bayan sa. Bisa la'akari da yanayin da ake ciki ne bankin duniyar ya rage hasashen da aka yi game da karuwar tattalin arzikin duniyar na bana zuwa kashi 2.4%.

Cikin rahoton, an ce, rage hasashen ya nuna cewa, karuwar tattalin arzikin kasashe masu sukuni ba ta kai yadda aka zata ba, haka kuma darajar wasu kayayyakin da ake bukatar su da yawa a sassan duniya ba ta farfado ba, yayin da aikin cinikayyar da ake yi a kasashe daban daban, da gudanar kudi tsakaninsu, su ma suna tafiyar wahainiya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China