Jiya Alhamis a birnin Paris, OECD wato kungiyar hadin gwiwa da raya tattalin arziki ta fitar da wani sabon rahoto game da hasashen karuwar tattalin arzikin kasashen duniya, inda ta yi hasashen cewa, a cikin shekaru biyu masu zuwa wato shekarar 2016 da 2017, adadin karuwar tattalin arzikin kasashen duniya zai kai kaso 3 cikin dari da kuma kaso 3.3 cikin dari, adadin ya ragu da kaso 0.3 cikin dari idan aka kwatanta da hasashen da kungiyar ta yi a watan Nuwamban bara.
Kungiyar ta yi hasashe cewa, tattalin arzikin kasashe masu ci gaba ba zai bunkasa cikin sauri ba, kuma tana ganin cewa, ci gaban zai bambanta da na kasashen da suka fi samun saurin ci gaban tattalin arziki. Misali, adadin karuwar tattalin arzikin kasar Barzil zai ragu da kaso 4 cikin dari a shekarar da muke ciki, yayin da a shekara mai zuwa kuwa, tattalin azrikin kasar ba zai ci gaba ba kwata-kwata.
Game da kasar Sin kuwa, hasashen kungiyar na nuna cewa, adadin ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin a bana zai kai kaso 6.5 cikin dari, yayin da a shekarar 2017 kuwa zai kai kaso 6.2 cikin dari, ko da yake babu wani banbanci sosai game da hasashen da kungiyar ta yi
Babbar masaniya a fannin tattalin arziki ta kungiyar OECD Catherine L. Mann ta bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu haka kasuwar kudi ta kasashen duniya ba ta gudana yadda ya kamata, kuma adadin busussukan da ake bin kasashen da suka fi saurin samun ci gaban tattalin arziki ya karu, duk wadannan za su kawo illoli ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. saboda haka ya zama wajibi kasashe daban daban su dauki matakai cikin gaggawa domin sa kaimi kan karuwar tattalin arziki a duk fadin duniya ta hanyar yiwa manufofinsu na kudi da tsare-tsaren tattalin arziki kwaskwarima. (Jamila)