in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya rage hasashensa game da yawan karuwar tattalin arzikin kasashen Afrika dake kudu da Sahara
2016-04-20 10:59:32 cri

Jaridar Vanguard ta Najeriya ta ba da labari a kwanan baya cewa, cibiyar bincike kan harkokin zuba jari a Afrika ta asusun IMF ta gyara rahoto game da hasashen da aka yi kan yawan karuwar tattalin arzikin kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara a shekarar 2016, inda ta rage shi da kashi 1 cikin dari, wato zuwa kashi 3 cikin dari, adadin da ke nan zai zama mafi kankanta a cikin shekaru 17 da suka gabata.

Daga cikin kasashen, cibiyar ta rage wannan adadi na Najeriya daga kashi 3.5 zuwa kashi 2 cikin dari, tana ganin cewa, yawan jarin waje da aka zuba a Najeriya zai ragu a sakamakon rashin tabbas kan manufar harkokin kudi a kasar, ko da yake farashin man fetur a duniya ya samu farfadowa, amma bai iya farfado da harkokin cinikayya da Najeriya ke gudanar da kasashen ketare kamar lokacin da ba. Ban da haka kuma, cibiyar ta bayyana cewa, yarjejeniyoyin musayar kudade da samar da rancen kudi da kasar Sin ta kulla tare da Najeriya za su taimaka ga kyautata yanayin harkokin kudi na kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China