A duk tsawon lokaci, Amurka na kanbama kanta a fannin fafutukar kare hakkin dan Adam, kuma ta sha zama malama a fannin na kare hakkin dan Adam, tare da yin shisshigi game da harkokin cikin gida na sauran kasashe, baya ga daga tutar kare hakkin dan Adam da take yi, don nuna karfin tuwo a duniya.
Tun daga farkon shekaru 70 na karnin da ya wuce, majalisar gudanarwar Amurka ta mika rahoto game da batun kare hakkin dan Adam na sauran kasashe ga majalisar dokokin kasar, kuma ta zargi wasu kasashe game da batun keta hakkin dan Adam na kasashensu.
A cikin 'yan shekarun nan, bayan da kafofin yada labaru na wasu kasashe da na Amurka ita kanta suka rubuta bayanai, kasashen duniya sun fahimta cewa, Amurka ta sha shaci fadi game da batun kare hakkin dan Adam na sauran kasashe, yayin da take yin rikon sakainar kashi game da batun kare hakkin dan Adam na kanta.
Matakan da ta ke dauka baya ga rashin dacewar su da tsarin mu'amala da shawarwari na girmama juna, da zaman daidaito a duniya, haka kuma ba za su yi amfani ba, wajen kyautata kare hakkin dan Adam ko da ga Amurkan ita kan ta. (Bako)