Minista a fadar gwamnatin Sudan Al-Rasheed Haroun, ya yi kira ga mahukuntan Sudan ta Kudu da su dauki matakan aiwatar da daukacin yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma ba tare da ware wasu gefe guda ba. Mr. Haroun ya ce, a nata bangare, Sudan za ta tabbatar da ta cika alkawarin ta na ganin an cimma nasarar zartas da yarjejeniyoyin 8, domin samun nasarar wanzar da zaman lafiya da lumana tsakanin sassan biyu.
A cikin watan Satumbar shekarar 2012 ne dai kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, suka sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi na warware wasu banbance banbance da ke tsakanin su, karkashin sanya ido daga kungiyar tarayyar Afirka ta AU.
Batun shata kan iyakokin kasashen biyu dai na sahun gaba cikin manyan kalubale da kasashen biyu ke fatan magancewa.(Saminu)