Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a ranar Litinin ya jaddada goyon bayan shi na ganin an samu zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu tare da kafa huldar zumunci tsakanin kasashen biyu.
Al-Bashir ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakoncin ministan harkokin wajen kasar Sudan ta kudu Barnaba Benjamin, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour ya bayyana wa manema labarai cewa, sakamakon ganawar shugahan kasar ya jaddada zurfin hulda dake tsakanin Khartoum da Juba.
A cewar al-Bashir, Sudan na aiki ita kadai kuma a tsakanin kungiyar gwamnatocin kasashen gabashin Afrika IGAD domin ganin an cimma zaman lafiya da daidaito.
Mr Ghandour ya kuma ce, takwaran shi na Sudan ta kudu har ila yau ya yi wa shugaba al-Bashir bayani a kan zaman lafiyar a kasar, sannan ya isar da sakon fatan alheri daga shugaba Salva Kiir Mayardit da ya shafi inganta zumnunci dake tsakani.
Ministan harkokin wajen kasar Sudan ta kudun a nashi bangaren ya jaddada muhimmancin zumunci tsakanin kasar shi da Sudan tare da kammala raba kan iyaka da aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwwa tsakaninsu.(Fatimah)