Kungiyar hada kan kasashen Afrika wato AU ta yi lale marhabun da ci gaban da aka samu bayan da aka kulla yarjejeniya a shekarar 2012 tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu karkashin jagorancin kwamitin aiwatar da yarjejeniyar na kungiyar wato AUHIP.
A ranar Larabar nan ne dai, gamayyar jam'iyyun siyasa da na tsaro na kasashen biyu wato JPSM suka karkare wani muhimmin taro na yini biyu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Shugabar kungiyar ta AU Nkosazana Dlamini-Zuma, ta fada a jiya Alhamis cewar, an samu matukar ci gaba wajen amincewa da aiwatar da yarjejeniyar ta shekarar 2012 tsakanin kasashen biyu.
Ta ce, a yayin karkare wancan muhimmin taro na ranar 13 ga wannan wata, wakilan dukkan bangarorin mahalartan taron sun amince da rattaba hannu kan jarjejeniyar zaman lafiya da kiyaye kan iyakokin kasashen.
Misis Dlamini Zuma, ta yaba wa shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, bisa amincewa da yarjejeniyar wadda ake sa ran wani mataki ne na samar da sulhu da juna tsakanin bangarorin biyu.
Sannan ta yaba wa jagorancin AUHIP bisa namijin kokari da kuma tsayawa kai da fata domin ganin an samu nasara wajen warware takaddama dake tsakanin kasashen biyu, kuma a cewarta, AU, a shirye take a ko da yaushe wajen daukar dukkanin matakai da za su tabbatar da zaman lumana tsakanin Sudan da takwararta Sudan ta Kudu.(Ahmad Fagam)