Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit ya ba da umurni ga sansanonin soji da su janye daga inda suke dake kan iyaka da kasar Sudan, kamar yadda gidan rediyon Tamazuj ta ruwaito.
Shugaba Kiir ya ce, ya kamata su janye zuwa a kalla mil biyar daga kan iyaka ta kudu da babban kan iyakan kamar yadda dokar ranar 1 ga watan Janairun 1956 ta tanada, da kuma bisa yarjejeniyar zaman lafiya ta shekara ta 2005.
Shugaba Kiir ya bayyana kudurinsa na daidaita dangantaka da Khartoum, yana mai cewa, akwai bukatar a yi aiki tare da juna kamar 'yan uwa a Khartoum, don a daidaita amincin da ke tsakaninsu.
Ya ce, gwamnatin shi za ta farfado da dukkan kwamitocin da wannan batu ya shafa, sannan a samar da zaman lafiya a kan iyaka domin al'ummar da ke zaune a wajen, inda ya nuna fatan shugaban Sudan Omar al-Bashir zai yi bayani cikin aminci dangane da daidata zumunci da bude kan iyakan domin sadarwa, ciniki da zumunci.(Fatimah)