in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Teodoro Obiang ya lashe zaben shugaban kasar Equatorial Guinea
2016-04-29 10:42:30 cri

Hukumar zaben kasar Equatorial Guinea , ta gabatar da sakamakon zaben shugaban kasar a jiya Alhamis. Sakamakon da ya nuna cewa, shugaban kasar mai ci, kuma shugaban jam'iyyar demokuradiyya mai mulkin kasar Teodoro Mbasogo, shi ne ya samu nasara da kuri'u da yawan su ya kai kashi 93.7 cikin dari, a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 24 ga wannan wata, lamarin da ya nuna cewa ya samu damar zarcewa a matsayin shugaban kasar, a wa'adin shekaru 7 masu zuwa.

Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa, yawan mutanen da suka yi rajistar jefa kuri'u a zaben ya kai 332,576, yayin da cikin wannan adadi mutane 309,158 suka jefa kuri'un su, wato kimanin kaso 93 cikin dari ke nan na daukacin wadanda suka yi rajista.

Mr. Mbasogo ya taba zama shugaban koli na rundunar sojin kasar Equatorial Guinea, ya kuma jagoranci kasar a shekarar 1979, kana a shekarar 1982 ya zama zababben shugaban kasar. Kana ya kuma lashe zabukan kasar na shekarun 1989, da 1996, da 2002 da kuma 2009. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China