in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bikin taya murnar cika shekaru 45 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Equatorial Guinea
2015-04-30 15:55:56 cri
An gudanar da bikin taya murnar cika shekaru 45, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Equatorial Guinea, a babban masaukin baki na Diaoyutai dake nan birnin Beijing a jiya Laraba 29 ga wata, inda shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Yu Zhengsheng, da shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo suka halarci bikin tare da gabatar da jawabi.

A cikin jawabinsa, Yu Zhengsheng ya bayyana cewa, a cikin shekaru 45 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Equatorial Guinea, jama'ar kasashen biyu sun nuna adalci da amincewa tare da girmama juna, kana bangarorin biyu sun nuna goyon bayan su da fahimtar juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu.

Shi kuwa a nasa jawabi shugaba Obiang, cewa ya yi a lokacin wannan ziyara tasa a kasar Sin, shugabannin kasashen biyu sun sanar da matakin inganta dangantakar dake tsakanin kasashensu, zuwa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa, da fahimtar juna, da cimma moriyar juna, da nunawa kasashen biyu makomar bunkasuwar dangantakarsu, tare kuma da kara sa kaimi ga hadin gwiwarsu.

Kaza lika shugaba Obiang ya bayyana cewa, kasarsa da kasar Sin abokai ne, kuma jama'ar kasashen biyu 'yan uwa ne. Inda cikin shekaru 45 da kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, bangarorin biyu ke taimakawa juna, kana jama'arsu na yin iyakacin kokari tare wajen samun ci gaba. Ya ce Equatorial Guinea na godiya ga kasar Sin bisa gudummawarta a fannin bunkasa tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasar Equatorial Guinea. Kana kasar tasa na burin kwazo tare da kasar Sin, wajen inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu a dukkan fannoni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China