Shugaban kasar Equatorial Guinea,Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a ran 14 ga wata, wanda yake ziyarar aiki a kasar.
Yayin ganawar su, Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya nuna cewa, Equatorial Guinea ta mai da kasar Sin matsayin sahihiyar kawa, kuma za ta nace ga matakin zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da fatan samun goyon baya daga kasar Sin a fannin masana'antu na zamani da sauyin hanyar da za ta bi ta fuskar tattalin arziki. Ya kuma bayyana fatansa na samun karin taimako daga kasar Sin wajen shimfida zaman lafiya da tsaro a kasar.
A nasa bangare Minista Wang Yi ya ce, Sin na dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma tana fatan kara amincewa da juna a fannin siyasa, zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Haka kuma tana son yin amfani da zumunci mai karko tsakanin kasahsen biyu don kawo moriyar juna da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin su a fannonin makamashi, masana'antu da dai sauransu. A sa'i daya kuma,Ministan harkokin wajen na Sin yayi fatan za'a samu karin hadin kai da kawo moriyar juna a fannonin aikin noma, amfanin teku da sauransu.
A kuma dai wannan rana, Mista Wang Yi ya gana da takwaransa na Equatorial Guinea Agapito Mba Mokuy, inda kuma yayin wani taron manema labaru da aka gudanar bayan ganawar ta su, Mista Wang ya ce ra'ayi mai dacewa da ya shafi yadda za a sauke nauyi gami da tabbatar da moriya ya kasance babbar manufar bai daya da Sin da kasashen Afrika suke kokarin aiwatarwa a yanzu. Ya ce Sin na fatan bin irin wannan ra'ayin da ya dace don inganta hadin gwiwa da kasashen Afrika, da samun ci gaban tattalin arziki, tare da cimma moriyar juna.
Har wa yau Mista Wang ya kara da cewa, goyon bayan juna, da taimakawa juna, tsakanin sassan biyu sun kasance wani yanayi na musamman ga kokarin bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen na Afrika.
Bugu da kari Wang ya ce Sin na fatan kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin ta da Afirka, tare da samun bunkasuwa tare, bisa ra'yoyin da suka dace kan yadda za a sauke nauyi gami da neman samun moriya. (Amina)