in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya ta karyata zarge zargen wata jaridar Amurka kan cin zarafin kananan yara
2016-05-12 10:46:15 cri
Gwamnatin Somaliya ta yi allawadai a ranar Laraba da wani rahoton jan hankali na jaridar Washington Post da ya nuna cewa jami'an tsaron kasar nada hannu dumi dumi kan ayyukan cin zarafin kananan yara.

A cikin wata sanarwa, hukumomin Mogadishu sun yi allawadai da wannan rahoto na wannan kafa mai fada aji ta Amurka, tare da bayyana shi a matsayin wani rahoton yaudara da karya.

Cikin sanarwa an ce, ana damuwa sosai kan rahoton da Washington Post ta fitar a ranar 7 ga watan Mayu, dake nuna cewa an take 'yancin kananan yara. A matsayin mambar da ta ratabba hannu kan yarjejeniyar MDD kan 'yancin kananan yara, kasar ta nuna damuwa sosai kan wadannan zarge zarge, kuma za ta gudanar da bincike yadda ya kamata domin tabbatar da hakikanin gaskiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China